Hausa WASSCE (PC 1ST), 2020

Question 2

Rarrabe tsakanin zuzau da ziza tare da misali uku-uku na kowanne.  

Observation

The question required the candidate to differentiate between fricative and voice with three examples each. The following explanations were expected to be captured by the candidates:

Zuzau:
Yanayi ne da gaɓoɓin furuci kan kusanci juna ƙwarai sai faɗin mafitar iska ya ragu ta yadda sai iskar ta gwada ɗan ƙarfi wajen ficewa. A dalilin haka, sai iskar ta samu wata ’yar tangarɗa wajen ficewar. Wannan tangarɗa ita ake kira zuza. Sautukan da ake furtawa ta wannan yanayi su ake kira zuzau. Daga cikin sautukan da ake samu ta wannan yanayin akwai:
            /f/                     /fy/
            /s/                     /sh/
            /h/                    /z/        

 

Ziza:
A nan tantani ne kan ja kaɗan sai maƙwallato ya tsuke yadda iska za ta nemi ficewa da ƙarfi. Dalilin haka sai tantanin ya riƙa karkaɗawa a samar da wata ’yar karkarwa wadda ake kira ziza.
Daga cikin sautukan da ake samu a wannan yanayin akwai:

                                    /b/        /ɓ/        /z/         /gy/
                                    /d/        /ɗ/        /ŋ/        /gw/
                                    /g/        /j/         /ɲ/
                                    /l/         /m/       /ɽ/
                                    /n/        /r/         /y/


Few candidates attempted the question and their performance was fair.