Hausa WASSCE (SC), 2022

Question 2

Yi bayani a kan:

 

(a)   Wasalin [e] da [oo]
(b)  Bambancin furucin [e] da [oo]

Observation

The question is on phonology, it required candidates to explain the articulation of [e] and [oo] in (a) and distinguish between them in (b). The response should be given as follows:

  1.       Bayanin wasula:

 

[e]   = Wasalin ƙofa ko gaba, na tsakiya, shimfiɗaɗɗe ko maras     
kewaya, gajere.
[oo] = Wasalin ƙurya ko baya, na tsakiya, zumɓurarre ko mai
            kewaya, dogo.

(b)       Abin da ya bambanta su:

[e]       Wasali ne na ƙofa ko gaba, shimfiɗaɗɗe ko maras kewaya,
             gajere.

[oo]     Wasali ne na ƙurya ko baya, zumɓurarre ko mai kewaya,
            dogo.

A taƙaice, sun bambanta dangane da:

  1. Matsayin harshe: - (gaba ko baya);

 

  1. Matsayin leɓɓa:  - (shimfiɗaɗɗe ko zumɓurarre ko mai kewaya ko

       maras kewaya);

  1. Tsayi:                 -  (dogo ko gajeren wasali).

                         Few candidates attempted the question and their performance was fair.