Hausa WASSCE (PC 2ND), 2021

Question 4

 

  1. Rarrabe tsakanin jumla mai aikatau da maras aikatau.
  2. Fitar da yankin suna da yankin bayani na waɗannan jumlolin:

 

  1. Malam Bala babban attajiri ne.
  2. Wani malami dogo fari ya sayi hula haɓar kada.

 

Observation

 

The question is on grammar and candidates were required to distinguish between the verb sentence and non-verb sentence in (a) and identify  noun and verb phrases of the sentences given in (b). The following explanation and examples are required from the candidates:

(a)  Rarrabewa:     
i    Jumla mai aikatau ita ce jumlar da ake samun kalmar aikatau a cikinta.

                                    Misali:
Audu yana karanta jarida kullum.
Tanko ya tafi makaranta.
Bala ya dawo daga umara.

ii  Jumla maras aikatau kuwa ita ce jumlar da ba a samun kalmar aikatau a cikinta.

Misali:
Shago jarumi ne.
Korau miskilin mutum ne.
Kande mata ce tagari.

(b) i Malam Bala/babban attajiri ne.
              (YS)              (YB)

ii  Wani malami dogo fari/ya sayi hula haɓar kada.
          (YS)                 (YB)

Many candidates attempted the question and their performance was good.