Hausa WASSCE (PC 2ND), 2021

Question 1

 

(a) Muhimmancin auratayya tsakanin ƙabilun ƙasar nan.

(b)  Yadda muka magance matsalar tsaro a garinmu

(c ) Rubuta wasiƙa zuwa ga malamin gona na garinku, ka bayyana masa yawan amfanin da ka samu a bana.

(d)Hanyar lafiya a bi ta da shekara.

(e ) “Maza sun fi mata iya mulki.” Mene ne ra’ayinka?

 

Observation

 

(a) This is an expository essay which required candidates to write on the importance of inter-ethnic marriage to this country. In doing so, they were expected to highlight some points which should include the following:

         Gabatarwa:
Ma’anar aure:

Alaƙa ce ta zaman tare tsakanin namiji da mace wanda ake yin sa da nufin samar da zuriya mai asali;

                      Yin wani bayani game da aure a taƙaice.

                       Gundarin jawabi:

                       Auratayya tsakanin ƙabilu tana:

Kawo haɗin kai;
Kawo zaman lafiya;
Kawo yarda da juna;
Ƙarfafa zumunta;
Kawo haƙuri da juna;
Kawo fahimtar al’adun juna;
Kawar da ƙyamar juna da tsangwama;
Ƙaruwar tattalin arziƙi
Sada zumunci;
Samar da al’umma mai mahanga ɗaya;
Yaɗuwar zuriya, da sauransu.

Kammalawa:

            Yin taƙaitaccen jawabi a kan abubuwan da aka tattauna a kai.

Candidates’ performance in this question was commendable.


(b) The question is on narrative essay and candidates were required to write on how security challenges were tackled in their town. Candidates were expected to enumerate measures taken to manage the situation as follows:

            Gabatarwa:

  Sunan garin;
  Ƙaramar hukuma;   
  Jihar da garin yake;
  Abin da ya kawo rashin tsaro;
  Matsalolin tsaron da aka fuskanta;

                        Gundarin jawabi:

                                     Matakan da aka bi wajen magance matsalar:
 Kafa ƙungiyoyin sa-kai da samar musu da kayan aiki;
 Bayar da horo ga jami’an tsaro da ƙungiyoyin sa-kai;
 Yin sulhu;
 Bayar da tallafi ga ƙungiyoyin sa-kai da jami’an tsaro na
             hukuma;
Kafa kwamitin tsaro a unguwanni;
Samar da fitillun kan hanya;
Samar da aikin yi ga matasa;
Samar da kyakkyawar alaƙa tsakanin jama’a da 
ƙungiyoyin sa-kai da kuma sauran jami’an tsaro. 
Wayar da kan jama’a game da tsaro;
Tabbatar da hukunci ga waɗanda suka aikata laifi;

                        Kammalawa:

                                    Kawo bayani a kan abubuwan da aka tattauna a kai, a taƙaice.       

Candidates that attempted the question performed well.

 

(c) This is letter writing. Candidates were required to write a letter to the Agricultural Extension Officer in their town explaining to him the outcome of the harvest they had this year. The following features of letter writing and points should be reflected:

 

            i    Sigar Wasiƙa:

Adireshin mai rubutu;
Kwanan wata;
Sallamar buɗewa (Zuwa ga);
Sallamar rufewa (Ni ne/ Ni ce/ Daga);

ii   Gundarin Wasiƙa:

Gonar da aka noma;
Yanayin ƙasar wurin;
Nau’in amfanin da aka shuka;
Tsarin da aka bi wajen noma gonar;
Yanayin damina a wannan shekara;
Yawan amfanin da aka samu;
Tasirin shawarwarin da ya bayar;
Matsalolin da aka fuskanta, da sauransu.

iii  Kammalawa:

                                    Godiya;
                                    Addu’a;
                                    Nuna jin daɗi;
                                    Fatan alheri;
                                    Tabbatar da haɗin kai/goyon baya, da sauransu.

Many candidates attempted the question and their performance was good.

 

(d) The question is proverbial which says “There is no hurry in life.” In attempting the question, the candidates were expected to state the meaning of the proverb, give examples of similar proverbs and narrate a story that will describe the proverb. The following points should be reflected and considered as relevant.

i   Ma’anar karin magana:

Karin maganar yana nuna cewa a bi rayuwa a hankali kuma duk abin da ake ganin shi ne mafita, to a bi wannan hanya komin daɗewa, don a gama lafiya.

ii  Karin magana kwatankwacin wannan:

            Sannu ba ta hana zuwa, sai dai a daɗe ba a zo ba.
            A daɗe ana yi sai gaskiya.
            Kowa ya kwana lafiya shi ya so.
            Ciki lafiya, baka lafiya.
            Sauri shi yake haifar nawa.
            Mai haƙuri shi yake dafa dutse.
            Da dariyar mai tauna yakan ƙoshi.
            Kwanci tashi kwana nesa.
Da sannu faifai zai shiga gora.
Zama lafiya ya fi zama ɗan sarki.

                        iii  Kawo labarin da zai dace da karin maganar.

                          Many candidates attempted the question and their performance was commendable.

 

(e) The question is an argumentative essay; it sought the opinion of the candidates on the motion: men perform better in leadership than women. In attempting the question, the candidates were expected to take a position and advance convincing reasons. The following features and points should be reflected:                                                                                   

Gabatarwa:

Taƙaitaccen bayani a kan mulki;
Fayyace ra’ayi:

                                    Maza sun fi iya mulki;

                                    Ko:

                                    Mata sun fi iya mulki;

            Gundarin jawabi (maza sun fi):

                        Kawo hujjoji:

                                    Zurfin tunani;
                                    Hangen nesa;
                                    Iya sarrafa jama’a;
                                    Ƙarfin hali;
                                    Jure wa kwaramnniya;
Kai zuciya nesa;
                                    Sauƙin mu’amala;
                                    Samun cikakken lokaci, da sauransu.

 

            Gundarin jawabi (mata sun fi):

                        Kawo hujjoji:

                                    Tausayi;
                                    Taka-tsantsan;
                                    Ɗaukar shawara;
                                    Tsoron aikata ba daidai ba;
                                    Sanin matsalolin iyali da rayuwa;
                                    Iya tattali;
                                    Sauraron jama’a, da sauransu.

            Kammalawa:

                        Yin taƙaitaccen bayani da jaddada ra’ayi.

Few candidates attempted the question and their performance was fair.