Hausa WASSCE (PC 2ND), 2020

Question 13

 

Bayyana halayen Hausawa a kan biyu daga cikin waxannan:

(a)Taimakon juna

(b)Nuna bajinta

(c)Gaskiya da tsare mutunci

Observation

Candidate was required to explain the philosophy of the Hausa people on any two of the norms stated above. The following explanations should be considered as relevant:

   (a) Taimakon juna:

A kawo bayani wanda zai qunshi muhimman batutuwa waxanda suke nuna halayen Hausawa dangane da taimakon juna kamar haka:

- Gudunmawar biki ko suna;
- Kyauta da sadaka da tukwici;
- Ajo;
- Xaukar nauyi;
- Taimakon marasa galihu;
- Tausaya wa marasa qarfi;
- Taimakon gajiyayyu;
- Kula da mara lafiya;
- Karrama baqi;
- Aikin gayya, da sauransu.

  1. Nuna bajinta:

 

A kawo bayani wanda zai qunshi halayen Hausawa masu nuna bajinta kamar haka:

- Haquri da juriya;
- Kula da iyali;
- Jarunta;
- Qwarewa a fannonin rayuwa daban daban kamar:

            - Tuqi;
            - Mulki;
            - Shari’a;
            - Kasuwanci;
            - Magana;
            - Farauta;
            - Girki;
            - Dambe ko kokowa;
            - Noma, da sauransu.
(c) Gaskiya da tsare mutunci:

A kawo bayani wanda zai nuna cewa Hausawa mutane ne masu gaskiya da tsare mutuncinsu a duk inda suke ta hanyar bayyana waxansu halaye masu gwada hakan kamar:
- Kunya;
- Kawaici;
- Riqon amana;
- Tsayar da magana;
- Cika alqawari;
- Ganin girma da mutunci mutane;
- Kara;
- Kyakkyawar shiga,
- Sanin ya kamata,
- Dattako, da sauransu

Candidates’ performance on this question was very good.