Hausa WASSCE (PC), 2023

Question 2

Bayyana bambancin furucin [d] da [y].

Observation

The question is on phonology, it required candidates to distinguish between the articulation of [d] and [y]. The response should be given as follows:

 

Furucin [d]:

kawo bayani ta yin la’akari da:

(a)       Gurbin furucinsa:

                 ɗan hanƙa ne;
                 bahanƙe ne.

 

(b)       Yanayin furucinsa:

                 tsayau ne;
                 ana tsayar da iska na ɗan lokaci idan za a furta shi.

 

(c)       Matsayin maƙwallato:

 

                 baƙi ne mai ziza;
                 maƙwallato yakan tsuke a lokacin furta shi.


            Furucin [y]:

kawo bayani ta yin la’akari da:

 

(a)       Gurbin furuci:

 

            ɗan ganɗa ne;
            baganɗe ne.

 

(b)       Yanayin furucinsa:

 

            kusantau ko kinin wasali ne;
            faɗin mafitar iska yana raguwa;
            mafurta suna kusantar juna.

 

(c)        Matsayin maƙwallato:

            mai ziza ne;
            maƙwallato yakan tsuke a lokacin furta shi.

Bambancinsu:

  1. Sun bambanta a gurbin furuci da kuma yanayin furuci.
  2. [d] bahanƙe ne, tsayau.
  3. [y] baganɗe ne, kusantau.

 

                           Few candidates attempted the question and their performance was poor.