Hausa WASSCE (SC), 2022

Question 10

 

                            Aboki, kiyayi ƙawa da kilaki,
                            Nemanta ba arziƙi sai fa hakki,
                            In ka ƙi kuɗinka sai daina auki,
                            Da ɗai bajimi bai abota da zaki,
                            Da ɗai gobara ba ta ƙyale haki.

 

  1. Wane salo aka yi amfani da shi a wannan baiti?
  2. Wane saƙo aka yi ƙoƙarin isarwa a baitin?

Observation

 

The question is on the book Waƙoƙin Hausa (Written Poetry). Candidates were required to mention the figure(s) of speech used in the stanza in (a) and state the theme in the stanza in (b). In doing so, they were expected to give the following response:

 

     (a)  (i)         An yi amfani da salon kamantawar fifiko a baitin kamar haka:

Da ɗai bajimi bai abota da zaki,
Da ɗai gobara ba ta ƙyale haki..

(ii)        Ana kuma iya ɗauka cewa, an yi amfani da salon siffantawa. Idan       aka ɗauki kilaki a matsayin zaki ko wuta, mai neman ta kuma a matsayin bijimi ko hakki domin a gwada haɗarin da yake tattare da mai neman ta.

                        Aboki, kiyayi ƙawa da kilaki,
                        Nemanta ba arziƙi sai fa hakki,
                        In ka ƙi kuɗinka sai daina auki,
                        Da ɗai bajimi bai abota da zaki,
                                    Da ɗai gobara ba ta ƙyale haki.

 

(b)       Marubucin waƙar ya yi ƙoƙarin jan hankalin mai sauraro da gargaɗinsa            
      game da haɗarin da yake tattare da neman kilaki, wato karuwa a    
       wannan baiti.

  1.  Jan hankali:

 

                      Aboki, kiyayi ƙawa da kilaki,
                      Nemanta ba arziƙi sai fa hakki.

  1. Gargaɗi:

 

In ka ƙi kuɗinka sai daina auki,
Da ɗai bajimi bai abota da zaki,
Da ɗai gobara ba ta ƙyale haki.

 

   (a)  (i)           An yi amfani da salon kamantawar fifiko a baitin kamar haka:

Da ɗai bajimi bai abota da zaki,
Da ɗai gobara ba ta ƙyale hakki..

(ii)        Ana kuma iya ɗauka cewa, an yi amfani da salon siffantawa. Idan       aka ɗauki kilaki a matsayin zaki ko wuta, mai neman ta kuma a matsayin bijimi ko hakki domin a gwada haɗarin da yake tattare da mai neman ta.

Aboki, kiyayi ƙawa da kilaki,
                        Nemanta ba arziƙi sai fa hakki,
                        In ka ƙi kuɗinka sai daina auki,
                        Da ɗai bajimi bai abota da zaki,
                                    Da ɗai gobara ba ta ƙyale haki.

 

(b)       Marubucin waƙar ya yi ƙoƙarin jan hankalin mai sauraro da gargaɗinsa            
      game da haɗarin da yake tattare da neman kilaki, wato karuwa a    
       wannan baiti.

  1.  Jan hankali:

 

                        Aboki, kiyayi ƙawa da kilaki,
                        Nemanta ba arziƙi sai fa hakki.

  1. Gargaɗi:

In ka ƙi kuɗinka sai daina auki,
Da ɗai bajimi bai abota da zaki,
Da ɗai gobara ba ta ƙyale haki.

 

 Candidates’ performance on this question was fair.