Hausa WASSCE (SC), 2019

Question 12

 

  1. Kawo kayan aiki biyar da wazamai suke amfani da su.
  2. Wace gudunmawa sana’ar wanzanci ke bayarwa ga jama’a?   

 

Observation

 

The question above is on Customs and Institutions (Al’ada), candidates were required to mention five implements that are used by local barbers in (12a) and state the contributions of barbing occupation to the community in (12b).

 

Thus:
(a)        Zabira;
            Aska;
            Sabulu;
Qoqo/kofi;
Qaho;
            Danqo;
            Ruwa;
            Dutsen washi;
            Fatar washi;
            ’Yar tsaga /Jarfa;
            Qoshiya / Dogari;
            Kalabai, da sauransu.

(b)      Sana’ar wanzanci ba qaramar gudunmuwa take bayarwa ga jama’a ba ta hanyoyi da yawa. Daga cikin gudunmuwarta akwai aski da gyaran fuska waxanda ba qaramin amfani suke da shi  ba a wajen jama’a. Idan aka ce a yau babu sana’ar wanzanci, yaya ake ganin mutane za su yi da gashin kansu da saje da gemu da hana qarya? Lallai abin ba zai yi kyawun gani ba.
            Wata gudunmuwar da sana’ar ke bayarwa ita ce  ta yin qaho domin magance ciwon mutuwar jiki da mataccen jini. Haka kuma takan taimaka wajen cire beli da yin kaciya da valli-valli. Har ila yau, wanzanci kan samar da magunguna ga jama’a kamar na kashe kaifi da maganin aska da na cututtukan jarirai da na manya.

              The candidates were expected to explain the following points:

  Tsabtar jiki;
Kyawun gani;
Ado;
Kiwon lafiya;
Riga kafi, da sauransu.

Candidates’ performance in this question was encouraging.