Hausa WASSCE (SC), 2021

Question 5

  1. Mene ne yankin bayani a cikin jumla?
  2. Gida nawa ya kasu?
  3. Kawo misali uku na kowanne a cikin jumla.

Observation

The question is also on grammar and the candidates were required to explain verb phrase in (a), list the classifications of verb phrase in (b) and give three examples of each in a sentence in (c). The answer should be as follows:

 (a)   Ma’anar yankin bayani:
Shi ne yake bin yankin suna a cikin jumla kuma shi ne yake ɗauke da ƙarin bayani a kan suna a cikin jumla.

(b)   Ya kasu gida biyu kamar haka:

  1. Mai aikatau
  2. Maras aikatau

 

(c) Misali a cikin jumla:
Mai aikatau:

Yaro ya zo.
Littafin ya yage.
Malam ya sayi kaza.
Yaran sun zo ɗazu.
Barau ya tafi kasuwa.
Larai ta rubuta wasiƙa.
Akuya tana shan ruwa.

  Maras aikatau:

Binta ce a gaba.
Ibrahim babban mutum ne.
Aliyu yaro ne.
Yaro sai iyayensa.
Binta kyakkyawa ce.
Motar nagagartacciya ce.
Ɗaliban masu hankali ne.

Candidates’ performance in this question was commendable